✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NDLEA ta kama Hodar iblis mai nauyin kilogram 12 a filin jirgin saman Abuja

Shi ne adadi mafi yawa na hodar iblis da NDLEA ta kama a filin jirgin a baya-bayan nan.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama wani mai fasakwauri da hodar iblis mai nauyinkilogram 12 a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

A safiyar Alhamis NDLEA ta cafke wani matashi da ke kokarin shigowa da kulli-kulli na kwayar Najeriya daga, Sao Paulo, kasar Brazil.

Kakakin hukumar a fiilin jirgin, Jonah Achema shine ya tabbatar da hakan ga ‘yan jarida a Abuja.

Ya ce, “An kunshe kwayar mai nauyin kilogram 12.05 a cikin ledar abarba da lemo da aka sanya a cikin wata jaka.

“Har ya dauki kayansa bayan saukarsa daga jirgi zai wuce wurin binciken NDLEA sai aka gano jakarsa daya na dauke abin da ake kargin hodar iblis ce”, inji kakakin.

Ya ce an cafke mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjojin da suka iso Najeriya daga Sao Paulo na kasar Brazil wadanda jirgin da suka shigo ya biya da su ta kasar Habasha.

“Ya ce wani mai suna Uche da wani abokinsa ya hada su ne a coci wata uku da suka wuce a Brazil ne ya ba shi sakon ya kawo Najeriya,” inji shi.

Wanda ya ba shi sakon, a cewarsa, ya ji shi ne yana magana da abokin nasa kan shirinsa na dawowa Najeriya.

Wanda ake zargin ya ce Uche ya kai masa jakar ce a filin jirgi a Sao Paulo dab da tashin jirgi don haka babu yadda zai iya tantance abin da ke cikinta.

Kwamandan NDLEA na filin jirgin, Kabir Sani Tsakuwa, ya ce kilogram 12.05 na hodar iblis din da aka kama shi ne mafi yawa da hukumar ta kama a baya-bayan nan.

“Mun yi alkawarin kama duk matafiyin dake da hannu a safarar kwayoyi kuma za mu ci gaba da sa ido”, inji Tsakuwa.