Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce jami’anta sun kama dalar Amurka miliyan 20 ta jabu.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta yi kamen ne a kan hanyar Abaji zuwa Lokoja a Abuja, babban birnin Najeriya.
- Ba za mu yarda sojoji su mulki Nijar tsawon shekara uku ba — ECOWAS
- Messi ya kafa tarihi a Inter Miami
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya tabbatar da cewa an samu kudin na jabu a cikin wata mota wadda ta taso daga Legas zuwa Abuja.
Mista Babafemi ya bayyana cewa an kama direban motar mai shekara 53.
NDLEA ta ce kwana guda kafin ta kama dalolin da take zargin na bogi ne, sai da ta kama wani mutum mai shekara 52 da kilo 2.2 na kwayar methamphetamine a wani samame da jami’an hukumar suka kai a kauyen Kabusa da ke Abuja.
Hukumar ta ce tun da farko ta kama mutumin da take zargi da kilo 20.75 na tabar wiwi a ranar 7 ga watan Yulin 2022, inda kotu ta bayar da belinsa, a yayin haka ne aka soma kama shi kan zargin wani laifin.
Haka kuma, NDLEA din ta kai wani samame a matattarar ’yan shaye-shaye biyu a unguwannin Dei Dei da Tora-Bora da ke Abuja, inda aka gano kilo 1.8 na rohypnol da kilo 1.2 na diazepam a ranar Laraba 16 ga watan Agusta.