Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen Jihar Neja ta ce ta kama buhu 125 na Tabar Wiwi daga masu safara a Jihar.
Kwamandan shiyya na hukumar a Jihar, Barista Haruna Kwatishe ne ya bayyan hakan lokacin da ya kai wata ziyara Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar.
- Jiragen yaki sun yi wa ’yan bindiga luguduen wuta a Sakkwato da Katsina
- Tun 2016 aka gano COVID-19 za ta bulla, amma aka yi sakaci
Ya ce ya kai ziyarar ne a wani bangare na kokarin hukumar na hada kai da ma’aikatu, hukumomi da bangarorin gwamnatin Jihar wajen yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar.
A cewar Kwamandan, “Muna gudanar da rangadi a fadin kasa don wayar da kan jama’a. burinmu shi ne mu tsaftace mutane daga illar shaye-shaye.
“Ko a kwanan nan, reshen rundunarmu ya sami nasarar kama buhu 125 na Tabar Wiwi daga hannun wasu masu kokarin yin safararta,” inji shi.
Barista Haruna ya kuma ce hedkwatar hukumar a Jihar na bukatar a katangeta don kare jami’anta daga hari, yana mai jinjina wa gwamnatin Jihar kan irin gudunmawar da take ba su.
Da yake nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka na Jihar, Mamman Musa, ya jaddada muhimmancin tallafa wa NDLEA a yunkurin da take yi na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.