Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta garmake wasu gidaje shida da shaguna 100 mallakin DCP Abba Kyari.
Kazalika, hukumar ta sanya wa kadororin nasa alamar jan fenti tare da garkame su don gurdanar bincike a kansu.
Daga cikin kadororin akwai wani gini mai hawa biyu a kan titin barikin sona na Giwa, wanda yake da shaguna kusan 100.
Idan ba a manta ba hukumar ta cafke Abba Kyari kan zargin kokarin bai wa wani jami’in hukumar cin hanci kan safarar hodar Iblis.
NDLEA ta kuma rufe wasu gidajen Abba Kyari guda shida a rukunin gidajen gwamnati da ke jihar, kwana biyu bayan cafke Mallinson Emmanuel Ukatu.
NDLEA ta cafke Ukatu kan zargin alaka da Abba Kyari wajen yin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasashen ketare.
Mista Ukatu na fuskantar tuhumar yin safarar kwayar tramadol har ta kudi biliyan uku.