Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), ta cafke wani jami’in tsaro bisa samunsa da yi wa daliban jami’ar Tarayya ta Jihar Ogun safarar miyagun kwayoyi.
Darektan Sashen Yada Labarai na Hukumar, Mista Femi Babafemi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin kasar.
- Amarya ta rasu a wajen daurin aure, ango ya aure kanwarta a take
- An harbe ’yan bindiga 14 da suka kai hari caji ofis a Binuwai
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Babafemi yana cewa, jami’in na wata hukumar tsaro ta kasa reshen Jihar Legas, ya shiga hannu ne a ranar Laraba, 15 ga watan Yuni.
Ya ce jami’in da aka kama an gano yana amfani da wani shagon matarsa a matsayin cibiyar gudanar da hada-hadarsa ta sayar da miyagun kwayoyi a wani yanki na Abeokuta, babban birnin Jihar.
Babafemi ya bayar da kididdigar miyagun kwayoyin da aka samu yayin simamen da aka kai shagon da suka hada da kwalaben Kodin 17, gram 22.26 na tabar wiwi, kwayoyin taramadol 230, gram 23.72 na flunitrazep da gram 48.16 na kwayar molly da sauransu.
Cikin sanarwar, Babafemi ya ce sun kuma kama wani dillalin miyagun kwayoyi a yankin Panteka na Jihar Kaduna tare da kilo 211.5 na tabar wiwi a kan hanyarsa ta zuwa Kano.
Haka kuma, ya ce sun kame wani dan Najeriya da ya dawo daga Pakistan a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas, dauke da gram 250 na muguwar kwayar nan ta heroin da ya boye a duburarsa.