✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA na son a daina ba ’yan kwaya zabin biyan tara a kotuna

Hukumar ta ce yanzu haka bukatar na gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta ce cire zabin biyan tara daga kudurin dokar hukumar zai karfafi yaki da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) wanda ya bayyana hakan, ya ce yanzu haka bukatar yi wa dokar hukumar kwaskwarima don cire sadarar biyan tarar na gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.

Buba Marwa ya bayyana hakan ne lokacin da yake kare kasafin hukumar na 2022 a gaban kwamitin Majalisar Dattijai kan yaki da miyagun kwayoyi a Abuja ranar Laraba.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar a Abuja.

Shugaban na NDLEA ya kuma ce ya ziyarci babban alkalin Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a John Tsoho, a kan batun wasu zabukan tara masu cike da ban dariya da alkalai ke ba masu ta’ammali da kwayoyin.

Sai dai ya ce cire sadarar da ta ba alkalai damar yanke hukuncin bayar da zabin tarar ga wadanda ake tuhumar zai taimaka wajen magance matsalar.

Da yake kare kasafin hukumar na Naira biliya 38, ya ce duk da yake kudin ba za su magance kafatalin matsalar ba, amma an sami ci gaba matuka in aka kwatanta da na baya.

Da yake nasa jawabin, Shugaban kwamitin Majalisar, Sanata Hezekiah Dimka, ya yaba wa Buba Marwa kan irin nasarorin da ya samu tun bayan karbar ragamar shugabancin na NDLEA.

Ya ce ko tantama babu, salon da bullo da shi wajen yaki da miyagun kwayoyi ya cancanci a yaba masa. (NAN).