Majalisar Wakilai ta ba wa Ministan Neja Delta Godswill Akpabio wa’adin sa’a 48 ya fallasa ‘yan Majalisar da suka karbi kwangiloli a Hukumar Kula da Yankin na Neja Delta.
Majalisar ta yi barazanar kai Akpabio gidan yari idan bai bayyana sunayen ‘yan majalisar da ya zarga da karbar kwangiloli a NDDC ba.
Akpbio ya yi zargin ne a ranar Litinin, lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban Kwamitin Majlisar kan NDDC da ke binciken zargin ruf da ciki a kan Naira biliyan 81.5 a hukumar.
Ya ce ‘yan majalisar sun karbi kwangiloli daga hukumar ta NDDC da ke karkashin ma’aikatarsa.
Wa’adin da Majalisar ya zo ne a lokacin zaman babban zaurenta na ranar Talata, bayan Shugaban Masu Rinjaye, Ndudi Elumelu ya samu goyon bayan takwarorinsa wajen kalubalantar zargin ministan da ya kawo hujjar zargin da ya yi.