Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), ta ce za ta sa kafar wando da kamfanonin sadarwar da ke kwashe data ko kudaden abokan huldarsa ba bisa ka’ida ba.
Shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta, ya ce dole a ba wa abokan huldar kamfanonin sadarwa kariya saboda kudadensu suke kashewa su sayi kati ko data don samun biyan bukata.
- Yadda ’yan bindiga suka karkashe juna a Katsina
- Sojoji mata 200 za su yi sintiri a hanyar Abuja-Kaduna
- Yadda za a kara hasken fata cikin kankanin lokaci
- An kara lokacin rajisatar lambar dan kasa da layin waya
“Duk da cewa an rage farashin data dole mu binciki kamfanonin mu gano masu zuke wa mutane kudade,” inji shi.
NCC a cewarsa, za ta yi hakan ne ta hanyar amfani da kwararrun da za su gano yadda kamfanoin sandarwa ke kwashe wa masu amfani da wayoyi data da kudade.
Ya ce tun da farko bincike ya gano kamfanoni sun kwashe wa masu amfani da wayoyi data da kudade ba bisa ka’ida ba ta hanyar tura sakonni.
Shugaban na NCC ya ce dole ne kamfanonin su bi ka’idoji da dokokin da hukumar ta shimfida.
Ya bayyana cewa Hukumar ta kirkiri wani bangare a shafinta na intanet inda mutane za su bayyana ra’ayoyinsu kan yadda suke amfani da data.
Da yake bayanin yayin karbar kambun karramawa daga kamfanin Mujallar ‘MoneyReport’, a ranar Alhamis a Abuja, Dambatta ya roki ’yan Najeriya da su kara hakuri zuwa lokacin da sakamakon binciken zai fito don daukar mataki na gaba.