Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta nuna rashin amincewarta da ƙarin kashi 50 da aka yi na kiran waya da data.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana ƙarin a matsayin matakin cutar da ’yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa.
Da yake magana a Abuja, Ajaero ya soki gwamnati da kamfanonin sadarwa saboda fifita riba a kan jin daɗin al’umma.
Ya ce ƙarin zai sa harkokin sadarwa su zama masu tsada, inda ma’aikata masu karɓar mafi ƙarancin albashi za su riƙa kashe kashi 15 na kuɗin da suke samu a kan sadarwa.
NLC ta buƙaci a dakatar da ƙarin nan take, tare da yin shawara da masu ruwa da tsaki don sake duba wannan matakin.
Ajaero ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar na iya shiga yajin aiki da kuma ƙauracewa ayyukan sadarwa idan gwamnati ba ta soke ƙarin ba.
“Ba za mu yarda da manufofin da ke ƙara talauci da rashin daidaito ba,” in ji Ajaero.
“NLC za ta yi tsayin daka tare da ‘yan Najeriya don ƙin amincewa da wannan ƙarin da ba a san dalilinsa ba.”