Kididdigar watan Dasumbar 2020 da Gwamnatin Tarayya ta fitar, ta nuna cewa adadin marasa ayyukan yi a Najeriya ya haura zuwa mutum miliyan 23.19.
Cikin rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar a ranar Litinin, ya nuna cewa adadin marasa ayyukin yi a kasar ya karu ne daga mutum miliyan 21.77 da aka samu a rubu’i na biyu na shekarar 2020 da ta gabata.
- Ramadan: Saudiyya ta fara rajistar masu ciyar da abincin bude baki
- Gwamnatin Tarayya ta sa ranar bude filin jirgin saman Kano
- An rufe makarantun Birnin Gwari bayan garkuwa da daliban firamare
A kididdigar da aka yi a kan rukunin shekarun haihuwa na masu ayyukan yi, an samu karuwa daga mutum miliyan 116.88 a rubu’i na biyu zuwa mutum miliyan 122.05 a rubu’i na hudu na shekarar 2020.
Masu ayyukan yi ’yan tsakanin shekara 15 zuwa 64 ya ragu daga mutum miliyan 80.29 zuwa miliyan 69.68 wanda hakan ya nuna an samu kashi 13.22 cikin 100 na adadin wadanda suka rasa ayyukan yi a tsawon wannan lokaci da aka gudanar da kididdigar a kai.
Kiyasin da aka yi ya nuna cewa akwai jimillar mutum miliyan 46.49 masu ayyukan yi a rubu’i na hudu wanda ya nuna raguwar kashi 20.6 cikin 100 na adadin da ake da shi a rubu’i na biyu na shekarar 2020.
A bisa wannan kididdigar da aka zakulo ta watan Dasumbar 2020, mutum miliyan 30.57 ne masu cikakken aikin yi sai kuma mutum miliyan 15.92 da suke aikin da bai wadace su ba.
Alkaluman sun nuna cewa Jihar Imo ita mafi yawan marasa ayyukan yi a kasar da kashi 56.6 cikin 100, sai kuma jihar Osun mai bi mata da kashi 11.7 cikin 100.
Ita kuwa Jihar Benuwe ta yi sauran jihohi fintikau da yawan masu ayyukan yi da bai wadace su ba da kashi 43.5 cikin 100 yayin da jihar Legas ta kasance da mafi karancin masu ayyukan yin da bai wadace su ba da kashi 4.5 cikin 100.
Ana iya tuna cewa, shekaru biyu da suka gabata ne Gwamnatin Tarayya ya bayyana fargabar karuwar adadin marasa aikin yi a Najeriya.