✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naziru dan Hajiya: Burina Kannywood ta zama masana’antar fim ta farko a duniya

Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru dan Hajiya furodusa ne, an haife shi a garin Jos, ya yi makarantar firamare a Jos, sannan…

Naziru Auwal wanda aka fi sani da Naziru dan Hajiya furodusa ne, an haife shi a garin Jos, ya yi makarantar firamare a Jos, sannan ya yi sakandare a Gombe, daga baya ya yi difloma da HND a kwas din ‘Business Administration and Management a makarantar Kano State Polytechnic, daga nan ya shiga harkar fim.
Yadda na fara fim
A lokacin da nake difloma sai yayata wato jaruma Jamila Nagudu ta ce ya kamata in samu wani abu da zan rika yi da zai taimake ni, bai kamata na tsaya sai an yi mini komai a rayuwa ba. Hakan ne ya sanya bayan na fara harkar fim sai na dauki bangaren shiryawa, inda na fara da fim din ‘karshen Furuci’. Fim din Jamila ne a karkashin kamfaninmu na JamNaz Entertainment.  Bayan na kammala difloma sai na shiga harkar fim tsundum.
Fina-finan da na shirya
Fina-finan da na shirya za su kai 20 zuwa 30. Kadan daga ciki sun hada da: ‘karshen Furuci da ‘Alkuki’ da ‘Gamo-Da-katar’ da ‘Halwa’ da ‘Da Kai Zan Gana’ da ‘Maja’ da ‘Mai Farin Jini’ da sauransu.
Fim din da na fi so
Na sha wahala a fim din ‘Alkuki’, domin na yi shi a Kaduna da kuma Abuja, abin da ya fi ba ni wahala shi ne, mun kwashe kwanaki biyar da mutane a Kaduna, sannan na sake kwaso su muka taho Abuja. Yadda na rika karakaina yayin daukar fim din ne ya fi ba ni wahala. Hakan ne ya sanya na fi sonsa fiye da kowane fim dina.
Burina
Burina shi ne, Kannywood ta zama masana’antar fim ta farko a duniya, sannan ina da burin zama jarumi da kuma darakta.
Yin fim maimakon aikin gwamnati
A kodayaushe mahaifina yana fada mini kada in yarda na dogara a kan aikin gwamnati, ya ce ko da zan yi aikin gwamnati, to na samu wani abu da zan rika yi. Ina da yakinin akwai lokacin da zai zo da za a ce mai matsayin karatu kaza ake bukata.
Abin da ya bata mini rai
Abin da ya faru a cikin fim din ‘Jamila Da Jamilu’ ne ya fi bata mini rai, dalili kuwa shi ne yadda Jamila (Jamila Nagudu) da Jamilu (Ibrahim Maishinku) suke zaune lafiya sai tsautsayi ya gifta har ya hadu da wata mata, a kullum na tuna hakan sai na ji raina ya baci duk da cewa kuwa fim ne, saboda nakan dauki fim da gaske.
Abin farin ciki
Nakan yi farin ciki a duk lokacin da na ji ana addu’ar Allah Ya daukaka harkar fim.