Sanadiyyar rashin aikin na’urar tantancewa ta sa masu kada kuri’a wadanda suka fito tun safiyar yau, basu sami damar kada kuri’a ba, sun nuna damuwarsu kan wannan lamari.
Wata majiya to shaidawa wakilin mu cewa ita na’urar zaben da aka tura yankin dama an shirya mata yin zabe a ranar 13 na wannan watan amma duk da dage zaben da aka yi a makon jiya ba a sauyawa na’urar ranar zaben na yau ba.
Wani mazaunin garin mai suna Yakubu Sabon gida, ya ce shi bai sami damar kada kuri’ar ba, sannan akwai runfunan zabe 49 a yankin akwai akalla masu kada kuri’a dubu 23 a yankin a mazabun Sabon gida kuma da gangan hukumar zabe ta sa na`urar zabe marasa kyau don a hana su yin zabe.
Jami`in wayar da kai na hukumar zabe ta Jihar Taraba mai suna Fabian Vwamhi ya ce, zai binciki lamarin sannan ya kira wakilinmu don yin bayani amma har yanzu bai kira ba.