Tun da Sallar Layya ta fara gabatowa Musulmai masu hali a Najeriya suka dukufa wajen sayen ragunan da za su yanka ranar Idi.
Ragunan dai iri-iri ne, sai wanda mutum ya ke so ko ya samu damar saya.
Aminiya ta zanta da shugaban riko na Kungiyar Masu Sayar da Dabbobi da ke Kano, Alhaji Bashir Sule Dantsoho, a kan nau’ukan ragunan da ake da su a kasuwanni.
Ya ce nau’ukansu sun hada da Dankasa da Uda da Balami da Gambarun Buzu da kuma Dan Sudan.
Ku biyo mu don jin yadda kowannensu yake:
Dankasa
- Yawanci gajere ne, ba shi da tsawo, kuma kahonsa a kife yake.
- A kan dade ana kiwonsa amma bai nuna girma sosai ba, saboda gajere ne kuma dukkan sauran nau’ukan sun fi shi girma a ido.
- Farashinsa ya kan kama daga N100,000 zuwa kasa.
Uda
- Launinsa akasari fari da baki ne, ko ja da fari, amma ana samun fari fat, ko ja.
- Yawanci daga Jamhuriyar Nijar ake kawo shi.
- Farashinsa ya kan kama tsakanin N250,000 zuwa N300,000.
Balami
- Shi kuma shi ya fi kowanne tsada, matukar an sami cikakke. Ya fi kowanne rago daraja.
- Sai dai za ka iya karade kasuwar dabbobi akalla 10 ba ka sami balami guda biyu ko uku ba.
- Ana kawo shi ne daga Tafkin Chadi zuwa kasar Kamaru.
- Farashin Balamin da bai wuce yaye ba ma ya kan kai kusan N50,000 zuwa N60,000, cikakke kuma a kan iya samun har na N350,000.
Gambarun Buzu
- Shi kala daya ne, yana saurin girma, kuma yana da daraja.
- Ana kawo shi daga Jamhuriyar Nijar, inda ake samo Uda.
- Farashinsa ya kan kama kamar kwatankwacin Uda ko Dankasa.
Sudan
- Kamar yadda sunansa ya nuna, tafiyayye ne, daga kasar Sudan ake kawo shi.
- Abin da ya banbanta shi da sauran shi ne yana da katuwar jela ba kamar ta sauran ba.
- Kusan kaso 90 cikin 100 na ragunan Sudan ba su da kaho.
- Farashinsa ya kan fi na Gambarin Buzu da Uda, Balami ne kawai ya fi shi tsada.