✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Natsuwa da addu’a ne masu kula da dabbobi ke yi – Shu’aibu

Shu’aibu Ali shi ne mai kula da dakunan zakuna biyun da ke Gidan Zoo na Kano ya ce duk da cewa ya dan sami horo…

Shu’aibu Ali shi ne mai kula da dakunan zakuna biyun da ke Gidan Zoo na Kano ya ce duk da cewa ya dan sami horo a makarantar kula da dabbobi ta garin Fanda da ke karamar Hukumar Albasu a Jihar Kano, amma yana samun kwarewa ce a aikin sakamakon zamansa a Gidan Zoo din inda yake aiki. “A kullum muna kara samun ilimin zama da dabbobi ta hanyar kula da su, na san halin kowane a cikinsu. Amma duk da haka addu’a da natsuwa su ne muhimman matakan da mai sana’a irin tamu ya kamata ya dauka, saboda wurin zaki misali yana da kofofi kusan hudu idan mutum zai ba shi abinci dole ya kula da duk kofar da zai bude ya tabbatar ya kulle ta bayanta kafin ya bude ta gaba. Idan mutum ya manta bai bi matakan nan yadda suke ba to komai zai iya faruwa.  Kuma akwai bukatar mutum ya hada da addu’a domin ya samu ya gama lafiya,’ inji shi

Ya ce ”Gidan zaki akwai daki akwai farfajiya, yayin da muka dauko nama sai mu bude kofar farko mu shiga, sai mu fara bude kofar farfajiyar yadda za mu killace su a farfajiyar idan muka tabbatar sun shiga can sai mu kulle wurin sannan mu bude kofar dakin sai mu shiga mu gyara musu mu shasshare mu gyara mu zuba musu ruwa da naman mu ajiye. Sanann sai mu fito daga dakin mu mayar da kofar mu rufe, sai kuma mu bude musu waccan ta farfajiyar sai su dawo ciki su ci gaba da cin abincinsu. Wani lokaci muna rufe farfajiyar wani lokacin kuma sai mu bar musu ita a bude don su samu walawa, saboda zaki ba ya son takura.”

Manajan Gidan Zoo na Sanda Kyarimi da ke Maiduguri, Malam Usman Lanu Maruma, wanda ya ce an kafa gidan sama da shekara 50 tun lokacin Turawa, gidan yana da ma’aikata masu kula da dabbobi daban-daban, kuma suna da dabbobi manya da kanana da suka hada da zakuna da giwaye da birrai da kuma tsuntsaye irin su jimina da sauransu.

Malam Maruma ya ce kowane nau’in dabba ana killace su ne a wata katanga da ake yi da karafuna ko a ce dakunan karafa da wayoyi, kuma suna da dabarun da suke bi don ba su abinci.

 Game da kiwon zaki, Malam Usman Maruma ya ce irin wadannan dabbobi da suke cin nama akwai tsaron da suke musu kuma dakinsu daban da na saura ake yi don gudun bacin rana. “Akwai karamin daki mai ciki da falo mai daukar zakuna 3 ko sama da haka to shi ma dakin an kewaye shi da karafuna da wasu kayayyakin tsaro da ko kana ciki ko kana waje za ka iya budewa, kuma masu kula da su akwai yadda suke ba su abinci da yadda ake kula da lafiyarsu, sannan wadanda suke ba su abinci sai mun tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya,” inji shi.

Ya ce, suna da dabarun tsare su daga cutar daga masu kula da su ko masu kai ziyara don kallo musamman a lokacin bukukuwan Sallah da Kirsmeti ko yawon bude ido na kowane lokaci.

Ya ce suna amfani da jami’an tsaro don hana turmutsitsi ko wuce iyakar da aka yarda su yi kallo, “Kuma a kullum muna gargadin masu ba su abinci su kula, idan mutum ba ya da natsuwa ba ma zai kusanci wurin ba,” inji shi.