Shararren tsohon dan wasan kwallon kafar Argentina, Diego Armando Maradona ya cimma nasarori da dama a rayuwarsa ta kwallo kafin rasuwarsa a ranar Laraba.
Maradona ya rasu ne bayan ya sha fama da ciwon zuciya; an sallame shi daga asibiti bayan an masa aiki a kwakwalwarsa.
- Tsohon dan wasan Ajantina Diego Maradona ya rasu
- Ba wanda zai yi rabin abin da Messi da Ronaldo suka yi a kwallo – Maradona
- Gasar kofin duniya
Maradona ya lashe gasar cin Kofin Duniya da kasarsa ta Argentina a 1986, inda ya zura kwallo 2 a wasan da suka buga da Ingila.
Ya buga wa Argentina wasa daga 1976 zuwa 1981 kuma ya buga wasanni 167, yayin da ya jefa kwallo 115.
![](https://i0.wp.com/hausa.dailytrust.com.ng/wp-content/uploads/2020/11/5b97d93e-d0c3-48c6-86e3-18c264ffee6b-maradona-600x337.jpg?resize=600%2C337&ssl=1)
Kungiyoyin da ya taka Leda
- Ya taka leda a kungiyar Boca Junior daga 1981 zuwa 1982, inda ya buga wasanni 40 kuma ya ci kwallo 28.
- A Barcelona, ya yi wasa daga 1982 zuwa 1984, ya buga wasanni 36 ya kuma zura kwallo 22.
- A kunungiyar Napoli ya taka leda daga 1984 zuwa 1991, ya yi wasanni 188, kuma ya jefa kwallo 81.
- Ya buga wasanni 26 a Sevilla daga 1992 zuwa 1994 kuma ya ci kwallo 5.
- A kungiyar Newell’s Old Boys daga 1993 zuwa 1994 ya buga wasanni 7 ba tare da ya zura kwallo ko daya ba.
- Daga nan ya sake komawa Boca Junior a 1995 zuwa 1997, ya buga wasanni 30, ya jefa kwallo 7.
- Baki daya a tarihin rayuwarsa ya buga wasanni 494, ya jefa kwallo 258.
- Gasar da ya lashe
- A shekarar 1981 Maradona ya lashe gasar Argentinean Championship na kasar Argentina
- A 1982 ya lashe gasar Spanish League Cup da kungiyar Barcelona
- A 1983 ya lashe gasar Spanish Super Cup da Barcelona
- A 1986 ya lashe gasar cin Kofin Duniya da kasarsa ta Argentina
- A 1987 ya lashe gasar Italian Cup da kungiyar Napoli
- A 1989 ya lashe gasar UEFA-CUP da Napoli
- A 1990 ya lashe gasar Italian Championship da Napoli
- A 1991 ya sake lashe gasar Italian Super Cup da Napoli
- Kyaututtukan da ya lashe
- Maradona ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasa na Kudancin Amurka (South American Footballer of the year) a 1979, 1986, 1989, 1990 da 1992.
- Gwarzon Dan Wasan Kukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA player of the century) a 1986.
- Kyautar kwallo mafi kyau a gasar cin Kofin Duniya na 1986.
![](https://i0.wp.com/hausa.dailytrust.com.ng/wp-content/uploads/2020/11/Armando-Maradona-367x367.jpg?resize=640%2C640&ssl=1)
Kungiyoyin da ya horar
- Maradona ya horar da kungiyar Textil Mandiyu a 1994
- Daga nan ya karbi ragamar horar da Racing Club a 1995
- Ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Argentina daga 2008 zuwa 2010
- Bayan shafe wasu shekaru ba tare da shiga harkokin wasanni ba, a 2011 ya karbi aikin horar da kungiyar Al-Wasl kuma ya ajiye aiki a 2012
- A 2013 zuwa 2017 ya karbi aikin mataimakin mai horar da kungiyar Deportivo Riestra
- Daga 2017 zuwa 2018 ya karbi kungiyar Fujairah domin horar da ita
- 2018 zuwa 2019 ya horar da Dorados de Sinaloa.
- Sai 2019 zuwa 2020, inda ya karbi horar da kungiyar Gimnasia de La Plata.
Masu harkar wasanni a fadin duniya suna jinjina irin hidima da rawar da marigayi Maradona ya taka a fagen harkar wasanni, musamman kwallon kafa.