A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Nasarawa United ya ziyarci Jihar Kaduna don samun horo a kokarin fuskantar kakar wasa mai zuwa.
Kulob din ya ce ya yanke shawarar zuwa Kaduna ne don ya samu horon da ya dace kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Kulob din ya ce ya yanke shawarar zuwa Jihar Kaduna ne don ya samu horo na kwanaki 10 inda ake sa ran zai kammala ziyarar a karshen makon gobe.
Tuni kulob din ya bayar da sanarwar yin tankade da rairaya ga ’yan kwallonsa kuma ana sa ran zai dauki zaratan ’yan kwallon biyar kafin a fara kakar wasa mai zuwa.