Gwamnatin Jihar Nasarawa ta mayar da almajirai masu yawon bara guda 40 zuwa jihohin su na asali.
Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta jihar, Halima Jabiru ce ta sanar da hakan a Lafiya ranar Litinin lokacin da take musu jawabi kafin a kwashe su zuwa jihohin nasu.
- Dan Majalisa ya ware N200m don samar wa almajirai 1,000 sana’o’i a Sakkwato
- Yadda gwamnoni ke facaka da biliyoyin Naira a zaben kananan hukumomi
A cewar ta, “Hakuncin da muka dauka na mayar da ku shawara ce da ilahirin Gwamnonin Arewacin Najeriya suka dauka don ganin sun kubutar da ku daga gararanbar da ku ke yi a kan tituna.
“Hakan ne ma ya sa Gwamna Abdullahi Sule ya samar da duk abinda ake bukata wajen ganin nasarar shirin, saboda kaunar da yake muku da kuma ganin kun sadu da iyayen ku da sauran ‘yan uwan ku,” inji ta.
Kwamishiniyar ta kuma ce an kama yaran ne yayin da suke kokarin kutsa kai domin shiga jihar daga Zariya ta jihar Kaduna.
Halima ta kuma koka da yadda ta ce wasu malaman kan boye almajiran idan an zo farautar su, sannan daga bisani su kyale su su ci gaba da gararanbar ba tare da daukar nauyin su ba.
Ta ce tuni suka gurfanar da irin wadannan malaman kuma za a yanke musu hukunci daidai da tanade-tanaden dokar da gwamnan jihar ya rattabawa hannu a kwanan nan.
A shekarar 2020 ne dai wasu daga cikin Gwamnonin Arewacin Najeriya suka sanar da hana almajiranci a jihohin su tare da mayar da dukkan almajirai zuwa jihohin su na asali.