✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nasarar Tinubu ta nuna yadda Arewa ke kaunarsa — Ganduje

Gwanduje ya ce Tinubu ya samu karbuwa a Arewa

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben fid-da gwanin dan takarar Shugaban Kasa a APC, ta nuna yadda mutanen Arewa ke kaunarsa.

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin sakon taya murna da ya aike wa Tinubu, ta bakin mai magana da yawunsa, Abba Anwar a ranar Laraba.

“Nasarar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben fid-da gwanin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC da aka kammala, ya nuna irin karbuwarsa a Arewa, a matsayinsa na mai hada kan ‘yan kasa,” inji shi.

Ya ce an gudanar da komai cikin lumana, ya kuma gode wa duk wadanda suka shiga takarar don inganta tsarin dimokuradiyya.

Ganduje ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan cewa zaben zai kara wa APC karfi a zaben 2023 ke kara karatowa.

Kazalika, ya yaba wa Gwamnonin Arewa bisa shawarar da suka yanke ta mayar da mulki zuwa yankin kudu da kuma yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da shawararsu.

“Wannan shawarar za ta hada kan dukkan sassan kasar nan.

“Gudunmawar da Shugaba Buhari ya bayar wajen tabbatar da cewa an kiyaye ka’idojin dimokuradiyya a wannan zaben, abun a yaba ne kuma abin koyi ne,” inji Ganduje.

Gwamnan ya yi kira ga duk wadanda ba su yi nasara a zaben fid-da-gwanin ba da su mara wa wanda ya yi nasara baya domin ciyar da jam’iyyar  da kasa baki daya.