✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasara tana tare da hakuri (1)

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. TaimakonSa da gafararSa muke nema. Kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu.…

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. TaimakonSa da gafararSa muke nema. Kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne.

Bayan haka! Ya ku bayin Allah! Ku sani, Allah Ya sanya hakuri ya zama tamkar wani ingarman dokin da ba ya tuntube, kuma tamkar takwabin da ba ya dakushewa, kuma tamkar wata rundunar da ba a taba karyawa, kuma tamkar wata ganuwar da ba ta rusunawa. Don haka hakuri da nasara ’yan uwan juna ne, kuma Danjuma ne da Danjumai, kuma duk mutumin da bai riki hakuri a matsayin makaminsa a addininsa da duniyarsa ba, to ya sani cewa, makiyansa sai sun fatattake shi. Makiyi ne na zuciya ko na Shaidan ne. Kuma babu wani karfi ga bawan da ba ya da hakuri. Kamar yadda babu shi babu cin nasara matukar ba ya da hakuri a yakinsa da yin gaba da abokin gabansa.

Allah Ta’ala Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri, kuma ku jure, kuma ku zauna cikin shiri, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta.”

Ya ku bayin Allah! Hakika shi hakuri igiyar talala ce ta mumini, duk inda ta je za ta komo gare shi. Kuma  shi hakuri ga mumini tamkar wata madogara ce da babu yadda ya iya sai ya dogara da ita. Babu imani cikakke ga wanda ba ya da hakuri. Duk sa’ar da imani ya yi karanci kuwa to sai ka ga ko da bautar Allah ma ta zama rabi-da-rabi. Ranar da gari ya yi dadi sai a yi, ranar da kuma abubuwa suka cabe sai a yi biris da ita.

Allah Ta’ala Ya ce: “Daga cikin mutane akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gaba, idan alheri ya same shi sai ya gamsu da shi, idan kuma wata musiba ta same shi sai ya juya baya, to wannan ya tabe duniya da lahira, wannan ita ce hasara mabayyaniya.”

Irin wannan bai samu komai a kasuwancinsa ba sai hasara mai girma da ya yi. Wadanda suka dace da kyakkyawar rayuwa sun same ta ce a dalilin hakurinsu. Don haka sun samu manya-manyan matsayi a dalilin godiyarsu ga Allah. Sun tashi sama da fika-fikin hakuri da na godiya ga Allah zuwa ga AljannarSa ta ni’ima. Saboda fadar Allah da Yake cewa:  “Wannan falala ce daga Allah, Yana bayar da ita ga wanda Ya so, Allah kuwa Ma’abocin falala ne Mai girma.”

Ya ku bayin Allah! Ku sani, shi hakuri halin cikakkun bayin Allah muminai ne, babu mai jure masa sai wanda Allah Ya karfafe shi. Annabawa da Manzanni (AS) su ne abin koyinmu a dukkan nau’o’in hakuri.

Imam Ahmad dan Hambal (Allah Ya rahamshe shi) ya ce:  “Allah Mai tsarki Ya ambaci hakuri sau casa’in a cikin Alkur’ani saboda muhimmancinsa.”

Sannan Allah Mai girma da buwaya Ya yabi masu hakuri a cikin littafinSa. Kuma Ya ba da labarin cewa ladar da zai ba masu hakuri, ta fi gaban lissafi, inda Yake cewa: “Hakika masu hakuri ne kawai ake cika wa ladarsu ba da lissafi ba.”

Kuma Allah Ya ce, Yana tare da masu hakuri da shiriyarSa da babban taimakonSa da bayyanannen budinSa. Ya ce: “Ku yi hakuri, hakika Allah Yana tare da masu hakuri.”

Kasancewar masu hakuri suna tare da Allah, ya sa suka rabauta da ni’imomin Allah na fili da na boye.

Haka kuma, bayan duk wadannan bayanai, Allah Mai girma da daukaka, Ya hada shugabanci a addini da hakuri da sakankancewa, inda Ya ce: “Kuma muka sanya shugabanni daga cikinsu (wato Banu Isra’ila) suna shiryarwa da umarninmu lokacin da suka yi hakuri, kuma sun kasance suna sakankancewa da ayoyinmu.”

Kari a kan haka, Allah Ya rantse a kan cewa hakuri alheri ne ga masu yin sa, inda Ya ce:

“Kuma lallai idan kuka yi hakuri, to babu shakka shi ne mafi alheri ga masu hakuri.”

Komai karfin abokin gaba, wallahi babu yadda ya iya da bawa mai hakuri da tsoron Allah. Allah Madaukaki ya ce: “Idan kuka yi hakuri kuka ji tsoron Allah, to makircinsu ba zai cuce ku da komai ba. Hakika, Allah Mai kewaye ne da saninSa ga abin da suke aikatawa.”

Sannan Allah Ya rataya rabautar bawa ga hakuri da jin tsoronSa. Sai Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri, kuma ku jure, kuma ku zauna a cikin shiri, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta.”

Kuma Allah Ta’ala Ya bayyana kaunarSa ga bayinSa masu hakuri. Ya ce, “Allah Yana son masu hakuri.”

Sannan ya yi wa masu hakuri albishir da abubuwa uku masu daraja fiye da abubuwan da bayi suke hassada a kansu a duniya, inda Ya ce: “Kuma ka yi albishir ga masu hakuri, wadanda idan wata masifa ta same su sai suce, mu na Allah ne, kuma mu wurinSa za mu koma. Wadancan (bayi) gafarar Allah ta tabbata a gare su da rahama, kuma wadancan su ne shiryayyu.”

Kuma babu mai tsira daga wuta ya rabauta da Aljanna face mai hakuri. Allah Mai girma da buwaya Ya ce: “Hakika Ni ina saka musu a yau saboda hakurinsu, hakika kuma su ne masu rabauta.”

Kuma Allah Ya kebance masu hakuri da godiya da amfanuwa da ayoyinSa inda Ya tantance su da wannan rabo mai girma, kuma gwaggwaba, har sau hudu a wurare daban-daban. Allah Ta’ala Ya ce: “Hakika game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan hakuri mai yawan godiya.”

Duba surorin Ibrahim da Saba’i da Lukman da Shura, za a ga haka.

Ku sani, ba wani abu ba ne hakuri face ka hana kanka yin raki da hana harshe kokawa da kuma hana gabbai make-make da kekketa sutura da makamantan haka.

Wani daga cikin nagartattun bayi ya ga wani mutum yana kai kukan matsalarsa ga dan uwa sa, sai ya ce da shi: “To ai kai ka kai karar wanda zai tausaya maka (Allah) wurin wanda ba zai tausaya maka ba (dan Adam).”

Wannan shi ya sa aka ce, mai kai kukansa ga dan Adam yana kai kukan Mai jinkai ne (wato Allah) wajen wanda ba zai jikansa ba.

Ya ku bayin Allah! Ku sani, kai kuka iri biyu ne.

Na farko shi ne, kai kuka ga Allah, Wanda wannan ba ya kore wa bawa hakuri. Kamar yadda Annabi Yakub (AS) ya yi lokacin da ya samu kansa cikin damuwar batar dansa Annabi Yusuf (AS), inda ya ce: “Ni fa kawai ina bayyana takaicina ne da bakin cikina zuwa ga Allah. Kuma na san wani abu daga Allah wanda ku ba ku sani ba.”

Duk da haka ya ce: “Na yi hakuri kyakkyawa.”

Na biyu shi ne, wanda yake cikin wani bala’i ya rika nuna damuwarsa da maganarsa ko da yanayinsa. Irin wannan salo ya saba wa hakuri, yana ma rusa shi.

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wata kyauta mafi yalwa da alheri da aka bai wa wani bawa irin hakuri.”

Shi hakuri tamkar linzami ne ga zuciyar dan Adam da zarar aka rasa shi sai zuciya ta bazama daji.

Ya ku bayin Allah! Ku sani, hakuri kashi uku ne, lura da abubuwan da suka rataya da shi.

Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto ne daga Birnin Makkah. Kuma za a iya samunsa ta tarho +2348038289761 ko imel: [email protected]