✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAPRI abar alfahari ce ga masu sha’awar kiwon dabbobi – Kwamandan Deffo

Kwamandan Makaratar Horar da Sajoji ta Deffo da ke Zariya, Manjo Janar Sani Muhammed ya bayyana Cibiyar Binciken Dabbobi ta Kasa (NAPRI) da ke Zariya…

Kwamandan Makaratar Horar da Sajoji ta Deffo da ke Zariya, Manjo Janar Sani Muhammed ya bayyana Cibiyar Binciken Dabbobi ta Kasa (NAPRI) da ke Zariya a matsayin cibiyar da ba ta da ta biyu mai kuma amfani ga kasa.

Kwamdan ya yi wannan bayani ne lokacin da ya kai ziyara cibiyar a kokarinsa na kulla dankon zumunci da hukumomi da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya da makarantarsa.                                                                                                                Janar Sani ya ce, NAPRI ta kasance abar sha’awa da alfahari ga masu sha’awar yin kiwon dabbobi tare da bunkasa dabbobi ta hanyar zamani.

A cewarsa, saboda muhimmancin da cibiyar ke da shi ta fannin tattalin arziki ya sanya ta zama mai matukar muhimmanci, Kwamandan ya ce, Rundunar Sojin Najeriya tana tunanin yadda za ta yi noma a kasar nan wanda ya ce, zai kai batun cibiyar ta NAPRI ga Babban Hafsan Sojojin Kasa don dubawa.

Da yake mai da jawabi, Daraktan Cibiyar  NAPRI, Farfesa Clarance A. Mawo Lakpini ya bayyana ziyarar a matsayin mai karfafa gwiwa kuma za ta karfafa zumuncinsu.

Farfesa Lakpini ya ci gaba da cewa, ko shakka babu ziyarar za ta tabbatar da irin manufofinsu na ci gaban kasa. Farfesa Lakpini ya ce babu wata cibiyar bincike da ta tsaya a kan manufar kafa ta kamar yadda NAPRI ta tsaya duk da matsalar kudi da cibiyar ta fuskanta a baya kamar sauran cibiyoyin Gwamnatin Tarayya.

Daraktan ya kara da cewa, NAPRI na bukatar kula ta musamman bisa la’akari da nau’in dabbobin da take kulawa da su a duk rana.