Nan gaba ake sa ran samun cikakken bayani kan yadda za a gudanar da aikin Hajjin bana yayin da kasar Saudiyya ta kammala nazarin kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar.
Ministan Yada Labaran Saudiyya, Dokta Majid Al-Qasabi ya sanar cewa mahukuntan kasar na bibiyar sababbin bayanai game da annobar sannan Ministan Ayyukan Hajji da Umrah da takwaransa na Lafiya za su yi bayanin matakan da aka dauka.
- Matashi ya haka daki a karkashin kasa saboda sabani da iyayensa
- Ku fito ku soki yunkurin kafa Biafra —’Yan Arewa ga manyan Ibo
“Ba ma son aikin Hajjin bana ya zama kafar yada cutar a kasar ko kuma ga duniya baki daya,” a cewar sanarwar.
Ya ce a sakamakon cutar COVID-19 din da take rikida, yana da matukar muhimmanci a yi nazari a kan yaduwa da illar da take haddasawa tare da gano hakikaninta.
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta yi aiki wajen inganta sashen aikin Hajji da Umrah, a daidai lokacin da ake ganiyar fama da annobar.
Hajjin bara da kuma dawo da Umrah sannu a hankali wanda aka faro tun Oktoba sun gudana ne bayan an yi tanadin tsare lafiyar mutane ta hanyar amfani da fasahar zamani a samar wa da mahajjatan dukkanin ababuwan da suke bukata da ma’aikatar ta samar.
Ma’aikatar ta kuma samar da ingantattun hanyoyin sufuri ta hanyar kafa wurare hudu na jigilar masu Umrah da mahajjata domin zuwa da kuma dawowa daga Babban Masallacin Harami.