✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da ’yan kwanaki za mu warware matsalar Frank Lampard -Kocin City Pelligrini

Kocin kulob din kwallon kafa na Manchester City da ke Ingila Manuel Pelligrini a ranar Talatar da ta wuce ne ya ce nan da ’yan…

Kocin kulob din kwallon kafa na Manchester City da ke Ingila Manuel Pelligrini a ranar Talatar da ta wuce ne ya ce nan da ’yan kwanaki masu zuwa kulob din zai warware matsalar dan kwallon tsakiyarsa Frank Lampard.
Frank Lampard, dan kimanin shekara 36, ya kasance a matsayin aro ne daga kulob din New York City na Amurka inda ake sa ran kwantaraginsa za ta kare a City ne a watan gobe.
Sai dai City za ta iya shiga matsala ganin daya daga cikin ’yan kwallonta Yaya Toure zai tafi gasar cin kofin Afirka da zai gudana a watan gobe kuma kulob din zai iya fadawa cikin matsala muddin ya kuskura ya bar Lamprd ya koma kulob dinsa a Amurka sannan Yaya Toure ta tafi gasar cin kofin Afirka.
Don haka ne kulob din ya fara tattauna yiwuwar dakatar da Lampard  don maye gurbin Yaya Toure a watan Janairu mai zuwa kafin a kammala gasar cin kofin duniya.
Da ma dai kulob din City ne ya mallaki kulob din New York City na Amurka, don haka akwai yiwuwar a kyale Lampard a City don ya cigaba da buga kwallonsa a matsayin na wucin-gadi.
A watan Janairu ne ake sa ran kulob din New York City na Amurka zai fara shirin tunkarar gasar rukuni-rukuni na Amurka da ake wa lakabi da Major League Soccer (MLS).