Gwamnatin Tarayya ta ce daga yanzu zuwa wata hudu masu zuwa za ta kawar da ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, shi ne wanda ya ba da tabbacin a lokacin jawabin hadin gwiwan kan tsaro tare da Ministan Tsaro da na Harkokin ’Yan Sanda.
- Yadda ambaliyar ruwa ta hana mayakan Boko Haram sakat
- An soma shari’ar matashin da ya yi sanadiyar yanke kafar daliba
Aregbesola ya ce: “Muna bai wa ’yan Najeriya tabbacin isashen tsaro da aminci, shi ya sa shugaban kasa ya umarce mu da mu sanar da ku cewa daga yanzu zuwa watan Disamba, kullun tsaro da aminci da za ku samu za su inganta.
“Abin da muke fama da shi yanzu ba wani abu ba ne face harin matsorata da aka tarwatsa maboyansu a wurare daban-daban, wanda suna yin haka ne domin a rika ganin cewa har yanzu da sauran karfinsu.
“Babbar manufarmu ita ce kawar da su gaba daya kasa sannan mu dawo da aminci a kowane taki na fadin kasar nan; kuma da izinin Allah hakan zai samu zuwa watan Disamba na wannan shekara.
“Za a ga da kamar wuya amma zai yiwu, domin mun shirya domin tabbatar da aminci da tsaro a kowane taki a fadin kasar Najeriya, kuma tuni aka bayar da umarnin yin hakan,” in ji Aregbesola.
A cewar ministan, bullar annobar COVID-19 na daga cikin abubuwan da suka kara dagula matsalar tsaro a Najeriya, duk kuwa da matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka.
“Amma za mu ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar Najeriya da kuma baki, domin tabbatar da aminci da kuma murkushe bata-gari da ke barazana ga al’umma a fadin kasarmu,” in ji shi.
Ta ci gaba da cewa, “Ba za mu huta ba har sai an samu cikakken aminci a Najeriya.”
Sauki ya samu —Lai Mohammed
Kalaman Ministan Harkokin Cikin Gidan sun zo ne bayan takwaransa na Ma’aikatar Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce a barazanar tsaro da Najeriya ta fuskanta a ’yan shekarun nan ita ce mafi muni tun bayan yakin basasa.
Lai Mohammed ya ce matsalolin tsaro a kasar sun hada da tayar da kayar baya da yin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da neman ballewa daga kasar da satar mai da fashi da sauransu.
Ya ce, “Tabbas wannan shi ne kalubale mafi girma da zaman lafiya da tsaron kasarmu suka fsukanta tun bayan yakin basasa a 1967 zuwa 1970.”
Sai dai ya ce hakan ya kusa zama tarihi domin matakan da gwamnati ta dauka a kan ’yan ta’adda da dangoginsu sun sa suna neman inda za su tsere.
“Wadannan wasu kalubale ne da ke iya buwayar kowace kasa, amma Alhamdulillahi da irin kokarin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
“Yanzu za mu iya cewa, barin in maimaita, mafi munin lamarin ya kau, tsaro da aminci na kara samuwa a hankali.
“Don Allah kada a juya maganata ko a yi mata mummunar fahimta. Ba za a rasa samun daidaikun matsalolin tsaro ba, amma ba su kai yadda aka rika samu a can baya ba.
“Yanzu ’yan ta’adda da ’yan bindiga da dangoginsu guduwa suke yi, amma ba za su iya guje mana ba, kamar yadda aka gani a kan maharan cocin Owo [wadanda daga bisani dubunsu ta cika].
“Za su iya ganin sun tsere, amma ba za su boye mana ba, kamar yadda ta faru kan maharan da suka kai wa sojojin rundunar tsaron shugaban kasa harin kwanton bauna a Abuja [su ma daga baya an hallaka su].”
Lai Mohammed ya kara da cewa, “Hakan ba ya nufin mun gama yaki da wadannan bata-garin.
“Abin da muke cewa shi ne sojojinmu da sauran jami’an tsaro sun shawo man manyan matsalolin tsaron da kasar nan ke fuskanta, yanzu an samu sauki sosai.
“Yanzu haka mun karya lagon ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga, sai guduwa suke ta yi, kuma ba za mu huta ba sai mun muttsuke su.”
Don haka ya yi kira ga jama’ar Najeriya da su ci gaba da mara wa jami’an tsaro baya, musamman ta hanyar fallasa bata-gari da ke cikinsu, domin a samu karin nasara a aikin jami’an tsaro na tabbatar da tsaro a kasar.
Haka kuma ya yi kira ga kafofin yada labarai da su taimaka wajen yada irin namijin kokari da nasarorin da jami’an tsaron Najeriya suke samu a kan ’yan ta’adda da dangoginsu.
Aminci na dawowa a Najeriya —Magashi
A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce sojoji na kara samun nasara wajen wakwar da ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas inda a yanzu sun kwace yawancin wuraren da a baya ’yan ta’adda ke yin yadda suka ga dama a yakin.
Magashi ya ce a yankin Kudu maso Kudu kuwa, jami’an tsaro sun shawo kan matsalar satar danyen mai da ke jawo wa Najeriya asarar Dala miliyan 500 a ’yan watannin da suka gabata.
Ya bayyana cewa yakin Kudu maso Yammacin Najeriya shi ne wurin da aka fi samun zaman lafiya idan aka kwatanta da sauran yankunan kasar.
Sai dai ya cee a can din kuma matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami da fasa bututun mai da ayyukan kungiyoyin asiri da fasakwauri su ne manyan kalubalen tsaro.
A cewar ministan tsaron, rundunar AWATSE da ke aiki a jihohin Legas da Ogun na samun nasara a ikinta na yakar masu fasa bututu da satar danyen mai.
Yakar ta’addanci da wuya —Ministan ’yan sanda
Shi kuwa Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, cewa ya yi, yaki da ’yan ta’adda abu ne mai sarkakiya.
Ya ce dole gwamnati ta yi hattara a yakar ta’addanci, saboda bata-gari na iya bin kowace hanya domin aiwatar da barnarsu, amma jami’an tsaro, dole su gudanar da ikinsu cikin bin doka.
Amma ya ce duk da haka ana samun saukin matsalolin tsaron, musamman a manyan hayoyin Abuja-Kaduna, Kaduna-Birnin-Gwari, Sakkwato-Zamfara da kuma Zamfara-Kaduna.
A cewarsa, rashin kawar da ayyukan ta’addanci gaba daya a yanzu na da alaka da yadda jama’a ba sa ba da rahoton bata-gari; sai kuma rashin adalci a bangaren shari’a wajen hukunta masu laifin ta’addanci.
Ya ce yawancin matsalolin tsaro da ake fama da su a yankunan kasar iri daya ne — ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami, mallakar haramtattun makamai, da sauransu, wadanda kusan babu jihar da ba a samun irin wannan.
Game da daukar karin ’yan sanda aiki sun bayan umarnin Shugaba Buhari a 2019, Dingyadi ya ce, kawo yanzu an dauki sabbin ’yan sanda sama da 30,000, ragowar 10,00 kuma za a dauke su a bana ko a farko-farkon badi.
Abin da zai haka cimma nasara — Kwararru
Sai dai masana a bangaren tsaro na ganin rashin adalci da talauci na iya kawo cikas ga cimma burin gwamnati na kawo karshe ayyukan ’yan ta’adda zuwa watan Disamban da ta yi alkawari.
Chukwuma Ume da kum Lawrence Alobi, kwararru ne a fannin tsaro, sun bayyan cewa karuwar tazara ta fuskar adalci tsakanin takalawa da masu kudi da karuwar talauci na iya kawo nakasu ga cim-ma burin gwamnatin.
Ume, wanda masanin inganta tsaro ne a Shirin Kawo Cigba na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP), ya ce baya ga amfani da karfin soji, akwai bukatar gwanatin ta magance wasu matsalolinta na cikin gida, ta hanyar yin sauye-sauye.
Ya ce duk da cewa amfani da karfin soji shi ne babbar hanya, amma rashin adalci kan jefa mutane cikin hadarin rashin tsaro.
Saboda haka, “Ya kamata ta tabbatar an yi gangami tare da aiwatar da irin wadanann tsare-tsare na adalci yadda ya kamata.”
Shi kuma Lawrence Alobi, wanda tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda ne a Abuja, ya bayyana abin da gwamnatin ta fada a matsayin “yaudarara kai”.
Ya ce, “Yaya ministan zai yi wannan maganar? Shi ne a fagen daga? Ina ganin wannan yaudarar kai ne kawai.
“Shi kansa ministan ya san ba zai yiwu ba. Shekara nawa ana yaki da ta’addanci, amma yanzu zai ce za a gama da matsalar kafin watan Disamba! Wannan dai sai dai a ce yana da buri.
“Ba na tunananin ya san hakikanin abin da ke kasa, wata kila kuma ya fadi hakan ne domin ya bai wa ’yan Najeriya kwarin gwiwa.”
Daga Sagir Kano Saleh, Maureen Onochie, Faruk Shuaibu & Idowu Isamotu