Shugaban Mara sa Rinjaye na Majalisar Dattijai, Sanata Eyinnaya Abaribe ya yi kira ga mata da su kara zage damtse wajen shiga a fafata da su a harkokin siyasa tare da neman hakkokinsu.
Ya ce idan ba su fito sun yi wa kansu da kansu yaki ba, babu wanda zai yi musu.
- HOTUNA: Yadda aka gudanar da bikin ba Sarkin Bichi sandar mulki
- An kama dan bindiga da makaman AK-47 guda 53 a Nasarawa
Tsohon Mataimakin Gwamnan na wadannan kalaman ne yayin wani taro da aka gudanar kan ci gaban mata ranar Asabar ta intanet.
Wata kungiyar ci gaba al’ummar Ibo mai suna Nkata Ndi Inyom Igbo (NNII) ce ta shirya taron ga mata.
Sanata Abaribe ya ce sannu a hankali, yawan matan da suke shiga harkokin siyasa ya ragu matuka in aka kwatanta da shekarar 1999.
A cewarsa, muddin ba a yi abin da ya dace ba, to za a iya kai lokacin da ko mace daya ba za a samu a Majalisar Dattijai ba.
Ya ce, “Duk lokacin da na yi kira da a kara ba mata dama, wai sai a ce wai me zai hana na sauka daga kejerar da nake kai na ba mace? Kun ji wani irin tunani. Saboda haka, dole ne ku tashi ku yi wa kanku yakin.
“Daga cikin abin da ya kamata kuma shi ne a kara yawan matan da ake nadawa mukamai a matakin Gwamnatin Tarayya.
“Abin takaici ne cewa tun daga 1999, kullum yawan mata masu rike da madafun iko raguwa yake yi. Ban san dalili ba.
“Watakila gwamnati mai ci ta fi wacce ta gabaceta tunani irin na mutanen da ne.
“Matukar muka ci gaba a haka, to za mu wayi gari babu ko mace daya a Majalisar Dattijai,” inji Sanata Abaribe.