✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nan ba da jimawa ba farashin 1GB na data zai koma N390 – Osinbajo

A yanzu haka dai ana sayar da gigabait daya tsakanin N1,000 zuwa N1,200.

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya na wani gagarumin shiri wajen ganin farashin gigabait daya na damar shiga intanet bai wuce N390 ba nan da shekaru uku masu zuwa.

A yanzu haka dai ana sayar da gigabait daya na datar tsakanin N1,000 zuwa N1,200, ko da yake farashin ya fi na wasu kasashe da dama rangwame.

To sai dai da yake jawabi yayin bude taron Masana Safayar Gidaje da Kadarori na Najeriya (NIESV) karo na 51 a Abuja, Osinbajo ya ce da zarar gwamnati ta kammala aikin shimfida na’urorin da take yi a kasa, farashin datar zai kara faduwa kasa warwas.

Ban da rage farashin kuma, Mataimakin Shugaban Kasar wanda Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Abubakar D. Aliyu ya wakilta ya kuma ce aikin zai kara saurin intanet a Najeriya zuwa megabait 10 a kowanne dakika.

Ya kuma ce Gwamnatin za ta shigo da ma’aikatan safayar wajen aikin shimfida na’urorin, musamman ta bangaren gine-gine.

Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban kungiyar ta NIESV, Emmanuel Okas Wike ya ce kamata ya yi gwamnati ta tsame hannunta kacokam daga harkar gina gidaje ta bar kamfanoni masu zaman kansu kamar yadda ta yi a bangaren sadarwa.

Ya ce gine-gine wata babbar hanya ce ta habaka tattalin arzikin kasa kuma kamata ya yi a shigo da kamfanoni masu zaman kansu cikinta ka’in da na’in.

%d bloggers like this: