Fitaccen malamin Musulunci a Jihar Sakkwato, Sheikh Bashir Ahmad Danfili, ya ce ’yan bindiga sun ciyar da karnukansu da naman direban wani makusancinsa da suka yi garkuwa da su.
Malamin ya bayyana haka a lokacin da yake rokon al’umma su taimaka da kuɗin fansar magidancin da iyalansa mutum biyar da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
A wani bidiyo da malamin ya yi, ya ce: “’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani makusancina, amma ba na son faɗin sunansa.
“A hanyarsu ta zuwa wani kauye ’yan ta’adda suka tare su suka yi garkuwa da su, suka kashe direbansu nan take, aka ba karnukansu namansa.
“Amma sauran suna nan ana tsare da su, ciki har da mutumin da matansa biyu da mahaifiyarsa da kishiyarta da kuma ’yar uwarsa.
“Masu garkuwar suna neman miliyoyin kuɗaɗe masu yawa, waɗanda ba mu da su.
“Ni malami ne ba ni da kudi, koyarwa kawai nake yi, ga shi kuma ’yan ta’addan sun ba da wa’adi da za a kai musu kuɗin idan ba haka ba za su kashe mutanen, ga shi kuma wa’adin ya kusa karewa.
“Na san za su iya, duba da abin da suka yi wa wani basarake kwanan nan da suka kashe shi.
“Don haka ina rokon al’umma da duk wanda zai iya taimakawa domin a biya kudin, a sako su.”
Dalibin Malam aka sace —Makusancu
Wani makusancin Dokta Bashir ya musanta maganar da ake yadawa a kafofin sada zumunta cewa iyalan malamin ’yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan malamin.
Labari ya karaɗe Soshiyal Midiya cewa an yi garkuwa da kishiyar mahaifiyar malamin da kanwarsa, sun kuma har an harbe direbansa har lahira.
Amma wani na hannun daman malamin, wanda aka sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa “gaskiyar magana wani dalibinsa ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
“Ana buƙatar kudi shi ne aka gaya wa malam da cewa ya nemi taimako domin a samu a ƙarbo dailibin.
“Ba iyalansa ba ne ko kishiyar mamarsa ba, cewa an harbi direbansa kuma, malam ya ƙaryata maganar da ake yaɗawa.
“Abin da ya janyo haka, da aka gaya wa malam, ganin dangin dailibin nasa na cikin damuwa sosai, kuma sun roƙi ya nema masu taimako a zatonsu in ya yi magana za a samu abin da ake buƙata da ’yan bindigar suka nema shi ya sa ya nemi taimako a wurin jama’a.
“Sai wasu suka juya lamarin cewa iyalansa ne ake rike da su, amma babu kane ko mama ko matar malam a hannun ’yan bindiga,” kalaman makusancin malam.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, bai daga wayar wakilinmu ba a lokacin da ya kira shi don jin ko suna da wata masaniya kan lamarin.
Ya ce wani dalibin malamin ne da kanwarsa da matarsa da kishiyar mahaifiyarsa da ’ya’yansa biyu aka sace.
Ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun harbi direban da yake dauke da su lahira.