✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naman biri(1)

Wasu Fulani ne su biyu, wa da kane suka je kiwo daji. Ba su dawo ba har abincinsu ya kare, yunwa ta kama su. Ganin…

Wasu Fulani ne su biyu, wa da kane suka je kiwo daji. Ba su dawo ba har abincinsu ya kare, yunwa ta kama su. Ganin haka sai babban ya farauto musu biri, suka gasa namansa suka cinye. Babban ya gargadi kanensa cewa idan sun koma gida, kada ya sake ya fada wa kowa labarin cewa sun ci naman biri. Kan haka suka koma gida, bayan rana ta gama dukansu, sun gaji likis. Suna isa gida sai kanen ya nufi randa domin ya sha ruwa amma bai iske kofi ba. Sai ya daga murya yana cewa: “Ina kofi yake, zan sha ruwa, domin mun ci maiko.” Jin haka sai babban ya buga masa harara. Shi kuwa kanen sai ya ce: “To, yaya kake hararata, ai dai ban ce mun ci biri ba, maiko na ce mun ci.”
Daga Jibril S. Ali Badawa Kano, 08095655514