✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Namadi ya naɗa mutanen Badaru kwamishinoni a Jigawa

Daga Ali Rabiu Ali Gwamman jihar Jigawa, Umaru Namadi ya bada sunayen jami’an tsohuwar  gwamnatin  Muhammad Badaru  a cikin ƙunshin mutanen da zai naɗa kwamishina.…

Daga Ali Rabiu Ali

Gwamman jihar Jigawa, Umaru Namadi ya bada sunayen jami’an tsohuwar  gwamnatin  Muhammad Badaru  a cikin ƙunshin mutanen da zai naɗa kwamishina.

Gwamna Namadi wanda tsohon mataimakin Gwamna Badaru ne ya miƙa sunaye 16 ga Majalisar Dokokin jihar Jigawa domin sahhalewa su zama kwamishinoninsa.

Daga cikinu mutane 12 sun yi aiki a gwamnatin Gwamna Muhammad Badaru.

Ango ya rataye kansa wata 4 bayan yin aure a Jigawa

Alhazan Jigawa sun sake dawowa Kano bayan jirgin da aka canza musu ya samu matsala

Mutanen sun haɗa da tsohon kwamishinan kuɗi Babagida Umar da tsohon kwamishinan ƙasa Aminu Kanta.

Akwai kuma tsohon kwamishinan albarkatun ruwa, Ibrahim Garba.

Tsohon kwamishinan ilimi Lawan Ɗanzomo, wanda tun 1999 ya ke kwamishina a Jigawa shi ma ya na cikin waɗanda aka tura sunansu majalisar.

Tsohon kwamishinan ƙasa Sa’id Ahmad da tsohon kwamishinan noma Auwalu Sankara su ma sun samu shiga.

Haka ma tsohon kwamishinan shari’a kuma Atoni Janar, Musa Aliyu na cikin ƙunshin kwamishinonin.

Akwai tsohon kwamishinan yaɗa labarai Muhammad Alhassan da tsohon babban sakatare a ma’aikatar lafiya da Muhalli Muhammad Kainuwa.

Sauran sun haɗa da mashawarcin gwamna Badaru kan harkokin siyasa Ahmed Garba da likitan gwamnan Badaru, Nura Ɗandoka.

Akwai kuma Hadiza Abdulwahab wacce ta yi kwamishinar mata a zamanin Gwamna Sule Lamiɗo.