Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa a ranar Laraba ya gabatar da kasafin kudin 2021 na naira biliyan 156 ga majalisar dokokin jihar domin tabbatarwa.
Aminiya ta ruwaito cewa, kasafin kudin ya haura da kashi 29 cikin dari idan an kwatanta da naira biliyan 124 da ya gabatar na kasafin 2020.
- Yadda Najeriya za ta bunkasa kasuwanci da fasahar zamani — NITDA
- An sa ranar nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
- An sake kama Naziru Sarkin Waka
Gwamna Badaru ya ce kasafin kudin da ya gabatar zai kawo ci gaba ga jihar kuma zai cimma manufofin gwamnatinsa na kyakkyawan shugabanci da kawo wa bangaren tattalin arziki sauyi da kuma kawo ci gaba.
Kasafin kudin ya fi ba da fifiko a kan harkokin ilimi, lafiya, ayyukan gine-ginen hanyoyi da wutar lantarki, noma da kiwo, ruwan sha da kuma ci gaban matasa.
Majalisar dokokin jihar ta yaba wa Gwamnan dangane da yadda yake kokari wajen gudanar da muhimman ayyuka na samar da ci gaba a jihar.
Kakakin Majalisa, Idris Garba Jahun, ya ce za a yi bitar kasafin kudin ta yadda ya dace domin hanzarta shigar da shi cikin doka.