Nakasassu daga fadin Jihar Oyo sun tare hanyar Ofishin Gwamnan Jihar saboda rashin daukar su aiki a bangaren da ba na koyarwa ba a Hukumar Ayyukan Koyarwa ta Jihar (TESCOM).
Masu zanga-zangar sun ce daga cikin sabbin ma’aikata 7,000 da aka dauka aiki a hukumar, nakasassu 149 kacal suka samu, kuma ya gaza kason da ya kamata a ba su.
- An cafke mai wankin motar da ya tsere da motar kwastoma
- Yadda masu karbar haraji suka ‘hallaka’ wani direba
- An ceto matar da ’yan uwanta suka kulle watanni 5 a daki
“Gurabu 350 ya kamata a ba mu, wato kashi 5% amma 149 kacal aka ba mu. Dalilinmu ke nan na zuwa nan. Muna son Gwamna ya sa baki a yi mana adalci”, inji wani daga cikinsu.
Masu zanga-zangar da suka mamaye babbar kofar shiga Sakatariyar Gwamnatin Jihar sun kuma ce ba za su watse ba sai gwamnan da kansa ya hallara a wurin ya saurare su.
Sun ce daukar matakin da suka yi ya zama dole saboda sun nemi aiki a matsayin ma’aikatan da ba masu koyarwa ba a TESCOM amma aka yi watsi da su.
Daya daga cikinsu, Adegbuyi Adekunle ya ce, “Muna zanga-zangar ne saboda ayyukan da ba na koyarwa ba a TESCOM.
“Yawancinmu ba a ba mu aikin ba, maimakon a ba mu mu da muke da tawaya, sai lafiyyayyu suka kwace aikin”, inji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa zanga-zangar ta haifar da cunkoson ababen hawa a Sakatariyar Gwamnatin Jihar da ke Agodi.
Wakilinmu ya lura cewa an tura jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda, DSS, Amotekun da NSCDS zuwa babbar kofar Sakatariyar don hana karya doka da oda.