Ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta kasa da aka fi sani da Super Eagles za ta kece-raini da takwararta ta kasar Afirka ta Kudu da ak wa lakabi da Bafana-Bafana a wasan sada zumunta a ranar Lahadi 30 ga wannan wata da muke ciki a Kano.
Za a gudanar da wasan ne a kokarin da Afirka ke yi na karrama zaratan ’yan kwallon da ke Nahiyar.
Daga cikin ’yan kwallon da za su halarci wasan daga bangaren Afirka ta Kudu sun hada da Brian Baloyi da Aaron Mokoena da Rudolph Seale da Cyril Nzama da kunton Fortune da Macbeth Sibaya da Naughty Mokoena da Maimane Phiri da Beanni McCarthy da Fani Madiba da kuma Jerry Sikhosana.
Ana sa ran magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar biyu za su kwarara birnin Kano don kashe kwarkatar ido don ganin yadda wasan zai gudana.
Najeriya za ta yi wasan sada zumunta da Afirka ta Kudu a Kano
Ana sa ran kungiyar kwallon kafa ta kasa da aka fi sani da Super Eagles za ta kece-raini da takwararta ta kasar Afirka ta Kudu…
