Gwamnatin Najeriya za ta tura sojoji guda 205 zuwa kasar Gambia, inda za su yi aikin tabbatar da samuwar tsaro zaman lafiya a can.
Tura wadannan sojoji 205 da Najeriya za ta yi zuwa Gambia na daga cikin manufar gwamnatin Najeriya na tabbatar da samuwar tsaro da aminci a fadin duniya.
- Harin bam ya hallaka mutane da dama a masallacin Afghanistan
- PDP: ‘Masu neman takarar Shugaban Kasa 2 sun yi asarar kudin fom dinsu’
Shugaban Ayyukan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar Olufemi Akinjobi, ya ce daga samun ’yancin Najeriya a 1960 zuwa yanzu, kasar ta tura sojojinta sama da 100,000 zuwa kasashen duniya, inda suka yi nasarar kammala ayyukan samar da tsaro guda 40.
Manjo-Janar Olufemi Akinjobi ya yi wannan bayani ne a taron bikin yaye sojojin da za a tura domin samar da tsaro a Gambia karkashin kungiyar ECOWAS, bayan horon da suka samu a Cibiyar Aikin Samar da Zaman Lafiya ta Martin Luther Agwai da ke Jaji, Jihar Kaduna.
Da yake magana ta bakin wakilinsa, Manjo-Janar Zakari Abubakar, Manjo-Janar Akinjobi, ya ce an kaddamar da aikin samar da tsaro na ECOWAS a Gambia ne domin kai dauki da kuma shawo kan rikicin da da biyo bayan zaben shugaban kasar na 2016.
A cewarsa, gudummawar dakarun ECOWAS a Gambia ta taka rawar gani wajen samar da daidaito da zaman lafiya, sakamakon kwarewarsu.