Asusun Lamuni na Duniya IMF, ya ce Najeriya na fuskantar barazanar fadawa cikin matsalar abinci a 2023.
IMF ya ce za a fuskanci wannan mummunar barazana saboda hauhawar farashi da kuma ambaliyar ruwa da tsadar taki a kasar.
A cewar kiddidiga hukumar NBS, hauhawar farashi a Najeriya ya kai maki 23.72 cikin 100 a watan Oktoban 2022, yayinda farashin wasu kayayyakin abinci ya karu daga kashi 50 zuwa 100.
IMF ya ce la’akari da wannan yanayi da ake ciki, farashin kayan abinci zai munana a 2023.
Sannan rahoton IMF ya ce duk da irin wadannan matsaloli, akwai kuma yakin Ukraine da ke shafar tattalin arziki da farashin kayan abinci.
IMF ta ce muddin baa tashi tsaye da bijiro da matakai ba, ’yan Najeriya da dama za su rasa abinci ko damar iya ciyar da kansu nan gaba kadan.
A makon da ya gabata ne Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce ’yan kasar miliyan 133 ke cikin talauci, kuma galibinsu ba sa samun ilimi da tsaro da kulawar lafiya.