✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta fara siyan fetur daga Nijar

An kulla yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da za ta bayar da damar jigila da ajiyar fetur tsakanin kasashen biyu. Sanarwar yarjejeniyar ta…

An kulla yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da za ta bayar da damar jigila da ajiyar fetur tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar yarjejeniyar ta fito daga Minista a Ma’aikatar Man Fetur na Najeriya, ta ce an shafe kimanin wata hudu ana tattaunawa kafin cimma matsayar yarjejeniyar tsakanin Najeriya da Nijar.

Minista Timipre Sylva, ya ce, “Wannan babban cigaba ne saboda Jamhuriyyar Nijar na da danyen man fetur mai yawan da take bukatar ta sayar, ita kuma Najeriya na da kasuwar sayar da shi”.

Ana sa ran nan ba da jimawa ba za a fara jigilar man fetur da dangoginsa da suka hada da kalanzir daga Nijar zuwa Najeriya.

Cif Sylva ya ce Najeriya da Nijar za su amfana da wannan yarjejeniyar da aka sanyawa hannu.