✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya za ta fara samar da fensir a cikin gida

Kwamitin Kimiyya da Kere-kere na Majlisar Dattawa ya bukaci a kara kudaden da aka ware wa Cibiyar Cigaban Ayyuka ta (PRODA) reshen Jihar Inugu, domin…

Kwamitin Kimiyya da Kere-kere na Majlisar Dattawa ya bukaci a kara kudaden da aka ware wa Cibiyar Cigaban Ayyuka ta (PRODA) reshen Jihar Inugu, domin fara sarrafa fensir a Najeriya.

Da take karbar bakuncin Babban Daraktanta cibiyar, Peter Ogobe, a ranar Laraba, Shugabar kwamitin, Sanata Uche Ekwunife, bayyana damuwa kan yadda gwamnati ta yi biris da bukatarta ta fara sarrafa alkaluman a gida.

Ta ce tun shekara ta 2016 suka bayyana wa ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu shirinsu na fara hakan, a wata ziyara ta musamman da suka kai masa.

Ekwinife ta ce duk da mabambamtan ra’a’yoyin da mambobin kwamitin majalisar ke da shi kan lamarin, sun nuna gamsuwa da aikin cibiyar.

“PRODA ta samu ci gaba, kuma za mu karfafa musu gwiwa don tabbatar da an kammala wannan aikin mai muhimmanci da ake da aniya.

“Burin majalisar ne ciyar da Najeriya gaba, musamman ta bangaren cigaban tattalin arzikinta.

“Muna da mutane masu dimbin ilimin fasaha da kimiyya da za su iya magance mana matsalolinmu na cikin gida,” in ji ta.

A karshe babban daraktan ya yabawa Sanatan bisa kokarin da ta yi na mayar da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire jigo ga tattalin arzikin Najeriya.