Masana sun ce sama da biliyan biyar daga cikin wayoyin salula biliyan 16 da aka yi kiyasin ana da su a fadin duniya za su zama tarkace a 2022.
Rahoton ya nuna duk da cewa wayoyin na dauke da wasu muhimman abubuwa da za a iya sake sarrafa su don amfani, amma haka za a yi watsi da su wanda hakan ka iya barazana ga lafiyar al’umma da muhalli.
- Harin bom ya kashe fasinjoji 9 a mota a Mali
- Jami’o’in Najeriya da suka yi zarra a duniya
- Kotu ta tura matashin da ya yi wa tsohuwa fyade zuwa kurkuku
Daya daga cikin masanan, Pascal Leroy ya ce, “Manyan wayoyi na daga cikin kayayyakin laturoni da muka fi maida hankali a kansu.
“Idan ba mu sarrafa kayayyakin cikinsu muka saka yi amfani da su ba, dole za mu rika zuwa mu nemo su a kasashe irin su China da Congo,” in ji shi.
Wayoyin da lamarin ya shafa wani dan kaso ne daga tarkacen kayayyaki lanturoni na ton miliyan 44.48 da ake yi duk shekara kamar yadda rahoto ya nuna.
Ya ce, wannan na faruwa ne yayin da mutane suka manta ko suka zabi ajiye wayoyin da suka lalace ko suka daina amfani da su a wurare daban-daban maimakon su mika su wajen gyara, ko kuma inda za a iya tattara a kwashe su zuwa kamfani domin sake sarrafa su.