Wasu kwararrun likitoci a Amurka na kokarin amfani da kimiyya wajen rage saurin tsufan mahaifa, domin ba wa mata tsofaffi damar daukar ciki.
Mataimakiyar Farfesa a bangaren binciken tsufa da ke jami’ar Buck a jihar Califonia, Jennifer Garrison ce ta bayyana hakan, ta cikin wani shiri da gidan talabijin na CNN, inda ta ce binciken ya kuma gano cewa matan da suka daina haihuwa daga shekara 40, na cikin hatsarin mutuwa da wuri da fiye da kaso 40.
- Mota ta kashe dan acaba da fasinjansa a hanyar Legas
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 10, ta raba wasu 2,538 da muhallansu a Adamawa
Haka kuma ta ce duk da cewa da zarar mace ta kai shekarun haihuwa 30 ko gab da haka, dukkan jikinta kan yi aiki fiye da ko yasuhe, in banda mahaifarta.
Garrison ta ce hakan na faruwa ne saboda a wannan lokacin ta fara nuna alamun tsufa.
A cewarta, matsalar ba a iya nan ta tsaya ba, domin da zarar mahaifar ta daina sakin sinadaran da ke sanya daukar ciki, tana hadawa har da wasu da ke taimakawa ingancin lafiyar jiki baki daya.
Haka kuma ta ce matsalar tsufan mahaifa ko ga lafiyayyar mace, na kara hatsarin kamuwa da ciwon zuciya da rashin bacci da mantuwa da kiba da sauran larurorin tsufa..
Sai dai ta ce da wannan kimiyya duk wadannan matsaloli za su zamo tarihi.