Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bullo da shirin bayar da tallafin iskar gas.
Babban Sakatare, Hukumar Kula da Asusun Man Fetur (PEF), Ahmed Bobboi, ya ce hakan zai daidaita farashin gas din girki, don tabbatar da an samu sauki.
- Sallah: Ranar Talata za a fara neman wata —Sarkin Musulmi
- Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono
- An dawo da dokar kullen COVID-19 a Najeriya
- An yi fashi a kusa da Fadar Shugaban Kasa
Ya shaida wa manema labarari cewa tallafin ya fara aiki, zai kuma taimaka wajen magance hauhawar farashin kayayyakin iskar gas.
Sai dai ya bayyana manufar na jiran zartar da kudirin Dokar Man Fetur (PIB) wacce za ta fayyace sabbin ayyukan PEF.
Ahmed Bobbai ya kuma jaddada cewa duk irin rawar da aka ba kwamitin tabbatar da daidaiton bangaren mai ne zai yi alkalanci gamen da matakin da za a dauka na gaba.
“Tun da yana aiki sosai a bagaren man fetur kuma gwamnati na son inganta amfani da gas, mun yi imanin cewa zai idan aka kawo shi bangaren gas, zai bunkasa tattalin arziki ta hanyoyi masu yawa,” inji shi.
“Muna kuma duba yiwuwar ganin ’yan kasuwar man fetur suna jigilarsa ta jirgin kasa saboda gwamnati na samar da layukan dogo a duk fadin kasar.
“Hakan zai rage kudin da suke kashewa da kuma takura wa tituna saboda gwamnatocin jihohi suna korafin cewa manyan motocin daukar kaya sun lalata hanyoyin, ina kuma ganin hakan zai rage kudin da gwamnatin ke kashewa wajen gyaran hanyoyin.”