Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta doke ta Sao Tome 6-0 a wasan neman shiga Gasar Kofin Afirka da suka kara ranar Lahadi a Uyo, Jihar Akwa Ibom.
Minti na 13 da fara wasa Super Eagles ta fara cin kwallo ta hannun Victor Osimhen, sannan Ademola Lookman ya ƙara na biyu minti na 14 tsakani.
- An yi jana’izar mamatan da hatsarin kwale-kwala ya kashe a Neja
- Kotu ta sake soke nasarar wani dan majalisar NNPP daga Kano
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne ɗan wasan Nottingham Forest Taiwo Awoniyo ya ƙara na uku a raga.
Najeriya ta ci kwallo na huɗu a bugun fenariti, kuma Osimhen ya zura a raga wadda ita ce cikon ta tara da ya ci a wasannin neman shiga Gasar Kofin Afirka.
Haka kuma shi ne ya ci na biyar na uku rigis a fafatawar, sannan Samuel Chukwueze ya ci na shida, saura minti huɗu a tashi daga gumurzun.
A wasan farko da Najeriya ta je gidan Sao Tome a karawar rukunin farko, ta yi nasarar cin 10 – 0 ne.