Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyya ga Shugaba Mohammed Bazoum na Jamhuriyar Nijar kan rasuwar mutum 69 a wani harin ta’addanci a kan iyakara kasarsa da kasashen Mali da Burkina Faso.
Da yake yin tir da harin da harin da ya ritsa da ran wani magajin gari a Jamhuriyar Nijar, Buhari ya ce harin babban koma baya ne ga kokarin da kasashen yankin Sahel ke yi na kawo karshen ayyukan ta’adanci.
- Yadda muka tsallake harin masu garkuwa sau 3 a rana daya
- Aminiya a kauyen su Shekau: Tun yana yaro fitinanne ne — Dagaci
“Wannan kidahumanci ne da bai dace da wayewar dan Adam ko hurumin ran dan Adam ba.
“Irin wannan cin kashin da ake yi kan mutanen haka kawai a wani wuri babbar barazana ce ga nahiyar Afirka, saboda haka akwai bukatar gaggawa na hadin kai tsakanin kasashen Afirka domin kashe matsalar ta’addanci daga tushenta,” inji Buhari.
Ya ci gaba da cewa, “A matsayinmu na shugabannin Afirka, ya zama dole mu tashi haikan mu gama da wadannan abokan gaban namu.
“Bai kamata a dauki matsalar ayyukan ta’addanci kamar sauran matsalolin tsaro ba, saboda kullum kara bazuwa take yi kamar wutar daji.
“Saboda haka ya kamata mu yi masa taron dangi mu murkushe wannan bala’in da ta hana harkokin yau da kullum da na tattalin arzikin kasashenmu sakat.
“Najeriya za ta ci gaba da bayar da gudummawa ga kasashen makwabata wajen yakar ta’addanci; Allah Ya jikan wadanda suka rasu, Ya kuma ba wa iyalansu hakurin rashi.” inji Shugaba Buhari.