✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta yi Allah-wadai da harbe dan kasarta a Ireland

Kungiyar dake rajin kare hakkin'yan Afrika a kasar Ireland, ta bukaci cikakken bayani game da kisan.

Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya a Kasashen Waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa wani dan Najeriya a kasar Ireland.

Ta yu kira ga mahukuntan Najeriya da su cikakken bincike game da kisan Mista George Nkencho mai shekaru 27 wanda ake zargin wani dan sanda a kasar ya harbe shi ranar 30 ga Disambar 2020..

Kakakin hukumar, Abdur-Rahman Balogun ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, inda ya bayyana kisan a matsayin rashin hankali.

Sai dai Dabiri-Erewa, ta ja hankalin ‘yan Najeriya mazauna Ireland da su bi lamarin a sannu, har zuwa lokacin da sakamakon bincike zai fito.

Ta kuma jajantawa iyalan mamacin da kuma al’ummar Najeriya mazauna kasar ta Ireland.

Tuni dai kungiyar dake rajin kare hakkin ‘yan Afrika mazauna Ireland (AANI), ita ma ta yi Allah wadai da kisan dan Najeriyar.

Kungiyar ta kuma bukaci cikakken bayani daga mahukunta kasar Ireland game da kisan da aka yi wa dan Najeriyar.