63: Oghenekharo Etebo ya canji Kelechi Iheanacho
62: Seychelles sun samu dama mai kyau, amma sun barar.
56: Ighalo ya zura wa Najeriya kwallo na uku daga fanareti
52: Kenneth Omerou ya tsayar da gaban Seychelles da kyar.
46: Najeriya na ci gaba da dannanSeychelles bayan an dawo hutun rabin lokaci.
45+1: Hutun rabin lokaci Najeriya 2 Seychelles 0
35: Najeriya ta zura kwallo na biyu. Chidozie Awaziem na zura kwallon bayan Iheanacho na bugo bugun tazara, inda ta buga sandar fos, sannan Chidozie Awaziem ya kwala mata kai.
31: Francis Uzoho ya cire kwallo na farko. Da alama Seychelles na shan wahala sosai.
15: Wannan ita ce kwallon Musa ta 16 a Najeriya.
14: Ahmed Musa ya zura kwallon farko. Ighalo ne ya bugo masa kwallon da ka, inda ya natsu ya jefa ta ragar Seychelles. Najeriya 1 Seychelles 0.
7: Najeriya ne ke taka ledar sosai. Da alama Najeriya tana neman ta fi karfin Seychelles.
‘Yan wasa:
Najeriya: Francis Uzoho; Leon Balogun, Kenneth Omeruo, Brian Idowu, Chidozie Awaziem, Wilfred Ndidi, Ogenyi Onazi, Kelechi Iheanacho, Ahmed Musa, Samuel Kalu, Odion Ighalo