Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Najeriya (NPHCDA) ta lalata allurar rigakafin cutar COVID-19 guda miliyan daya da dubu sittin da shida da dari biyu da goma sha daya.
Allurar rigakafin da aka lalata samfurin AstraZeneca ne da suka daina aiki, kuma an lalata su ne da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).
- COVID-19 ta kama mutum 4,035 a Najeriya
- Babu abin daga hankali a sabon nau’in Coronavirus na Omicron —Biden
Da yake bayani a wurin lalata su a Abuja, Babban Sakataren NPHCDA, Faisal Shuaib, ya ce an janye alluran daga wuraren da amfani da su ne tun kafin cikar wa’adinsu na daina aiki.
A cewarsa, hakan ya nuna irin kyakkyawan tsarin da Najeriya ta yi wa shirinta na bayar da allurar rigakafin ctuar.
A cewarsa: “Aikinmu na bukatar rikon amana, wanda kuma babban nauyi da ’yan Najeriya suka dora mana, saboda haka muke yin duk mai yiwuwa domin rike amanar da ta sa a yau muke lalata wadannan alluran rigakafi da suka daina aiki.
“Tun a lokacin da aka kawo mana su a watannin baya, mun san cewa ba masu tsawon kwana ba ne, amma kuma muna cikin wani yanayi da samun alluran rigakafin COVID-19 ke da wahala saboda kowace kasa ta kanta take yi, musamman masu samar da ita.”
Ya ce duk da haka kawo yanzu an yi wa mutum miliyan 10 allurar rigakafin kafin su daina aiki.
“Da mun tsaya jira sai lokacin da alluran suka samu a ko’ina, da watakila har yanzu babu dan Najeriyar da aka yi wa ita,” kamar yadda ya bayyana.
A cewarsa hakan da aka yi ya rage wa Najeriya asarar Dala miliyan 40 a wasu bangarori na kiwon lafiya.