Shugaban jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus ya ce Najeriya ta lalace a mulkin jam’iyyar APC.
Secondus ya bayyana hakan ne a Karamar Hukumar Sagbama, Jihar Bayelsa yayin ba da tuta takara ga Henry Seriake.
- Sanata Elisha Abbo ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC
- Mutum 9 sun shiga hannu kan kisan Shugaban APC na Nasarawa
Ya ce komai ya tabarbare a kasar ciki har sa tattalin arziki a mulkin APC.
Shugaban na PDP ya kara da cewa hanya mafi dacewa ita ce talakawa su zabi mutanen da suka dace domin jagorantar su a majalisa.
Secondus ya jagoranci ’ya’yan jam’iyyar ta PDP wajen nuna alhininsu kan kisan manoma 43 da Boko Haram ta yi a Zabarmari, Jihar Borno.
Shugaban jam’iyyar ya kuma ce ya kamata Manyan Hafsoshin Tsaro su san cewa Najeriya ta lalace a karkashin jagorancinsu.
Sannan ya sake jan hankalin Shugaban Kasa a kan kawo karshen ta’addancin da ake yi a jihohin Borno da Katsina.
A cewarsa, ya kamata jama’ar Najeriya su kaurace wa sake zabar APC a 2023, su yi koyi da irin abin da ya faru a kasar Amurka.