Wani rahoto da Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta fitar ya nuna cewa kasar nan ta fita daga masassarar tattalin arzikin da ta fada a ciki.
Rahoton ya ce tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu’i na biyu na bana, idan aka kwatanta da rubu’i na biyu na bara.
Hakan yana nufin cewa girman bunkasar da aka samu ya haura wanda aka samu a rubu’i na biyu na bara da kashi 2.04 cikin 100.
Tattalin arzikin kasar nan ya samu wannan tagomashi ne bayan da ya kwashe rubu’i biyar yana ci gaba da masassara.
A lokacin da tattalin arzikin yake bunkasa, ana fitar da gangar danyen mai miliyan 1 da dubu 840 a kowacce rana, inji Hukumar NBS.
Hukumar ta ce, baya ga man fetur, harkar noma da inshora da gas da lantarki na cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin.
Sai dai wani masanin tattalin arziki, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya shaida wa BBC, cewa tattalin arzikin kasar nan yana tafiyar hawainiya duk da Hukumar NBS din ta ce kasar nan ta fita daga masassarar tattalin arzikin da ta yi fama da shi.
Masanin ya ce idan tattalin arziki yana bunkasa da kashi daya ko biyu ko uku, to hakan na nufin yana tafiyar hawainiya ke nan, “wanda shi ma matsala ce.”
Farfesa Garba Sheka ya ce idan zai kwatanta yanayin da ake ciki, shi ne tamkar marar lafiya ne ya je asibiti aka yi masa gwaji, tare da ba shi magani.
“An karya lagon cutar, amma akan dauki lokaci kafin mutum ya murmure ya yi karfi,” inji shi.
Ya ce a halin yanzu matasa marasa aikin yi da mutane da ke cikin matsin rayuwa, ba a yau ko gobe ne za su fara jin sauki ba. “Samar da ayyukan yi, abu ne mai wahala domin kuwa akwai akalla matasa miliyan 25 da ba su da aikin yi (a kasar nan),” inji Sheka.
Masanin ya ce wajibi ne gwamnati ta tallafa wa matasa ta hanyar koya musu sana’o’in dogaro da kai da kuma ba su jari. Ya ce hakan ne hanya mafi dorewa domin kuwa gwamnati ba za ta iya samar musu aiki ba, kuma dogaro da daukar aiki daga kamfani ba koyaushe ake samun nasara ba.
“Amma mutum ya dogara da kansa, wannan ita ce hanya mafi dacewa,” inji shi.