✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta doke Ghana a wasan sada zumunta

Tarihi ya nuna sau 56 Najeriya da Ghana suka kara a fagen kwallon kafa.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke takwararta Black Stars ta Ghana a wani wasan sada zumunta da suka fafata yau Juma’a a kasar Morocco.

An dai tashin wasan ne 2–1, inda Najeriya ta yi galaba a kan makwabciyarta da ke Yammacin Afirka.

Dan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci kwallon farko a bugun fenariti a minti na 38, sannan a minti na 84 kuma Ademola Lookman ya zura tasa kwallon.

Ghana ta ci kwallonta ne da bugun fenariti ta hannun dan wasanta Jordan Ayewa gab da ana kusan tashi a wasan.

Daya daga cikin ’yan wasan bayan Ghana ya Jerome Opoku ya samu jan kati a minti na 56 da soma wasan.

Haduwar kasashen biyu na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan kammala Gasar Kofin Nahiyyar Afirka na AFCON da aka yi a Ivory Coast wacce ta lashe kofin.

Najeriya ta kai wasan karshe a gasar yayin da aka cire Ghana tun a zagayen rukuni-rukuni, lamarin da ya yi sanadin korar mai horar da ‘yan wasan kasar.

Tarihi ya nuna sau 56 Najeriya da Ghana suka kara a fagen kwallon kafa a gasa daban-daban da wasannin sada zumunci.

Ghana ta doke Najeriya sau 25 yayin da ita kuma Najeriya ta doke ta sau 12.

Sauran wasannin an tashi ne babu ci tsakanin kasashen biyu wadanda makwabtan juna ne a yankin yammacin Afirka.

Haduwa ta karshe da suka ita ce a wasan cin kofin duniya a 2022 da aka yi a Rasha inda Ghana ta fitar da Najeriya daga gasar.

Fitaccen dan wasan Najeriya Victor Osimhen bai samu zuwa wasan ba saboda rauni da ya ji.

Kazalika, Taiwo Awoniyi da Tyronne Ebeuhi da Gabriel Osho duk ba su samu halartar wasan na sada zumunci ba.

A bangaren Ghana, fitaccen dan wasan kasar Thomas Partey, shi ma bai samu zuwa wasan ba.