✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Najeriya ta cire dokar gwajin COVID-19 ga matafiya kwata-kwata

Gwamnati ta ce tana bai al'umma shawara kan kowa ya tabbatar ya yi cikakken riga-kafin cutar.

La’akari da raguwar yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta dage dokar yin gwajin cutar ga matafiya masu shigowa da ficewa daga kasar kwata-kwata.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Yaki da COVID-19, Boss Mustapha ne ya ba da sanarwar hakan ranar Litinin.

Ya kuma ce gwamnatin ta kuma dage dokar tilasta amfani da takunkumin rufe fuska ga jama’a.

A cewarsa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da dage dokar ne bayan la’akari da nasarar da kwamitinsa ya samu wajen taikata yaduwa cutar a kasa.

Sanarwa ta ce, daga yanzu an dakatar da yin gwajin COVID-19 ga matafiyan da ba su yi cikakken rigakafin cutar ba.

Da wannan matakin dai yanzu, babu bukatar fasinjoji su sanya bayanan shaidar yin rigakafin COVID-19 a shafin NITP, in ji sanarwar.

Sai dai, sanarwar ta ce ana shawartar jama’a, wadanda ba su kammala yin rigakafin ba da ma wadanda ba su yi ko daya ba, kowa ya kokarta ya yi cikakken rigafin cutar.