✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya na zargin Twitter da hannu a fafutikar kafa kasar Biyafara

Hakan dai na zuwa ne bayan shafin ya goge wani sako da Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana da shakku kan aikace-aikacen dandalin sadarwa na Twitter kan alakarsa da masu neman kafa kasar Biyafara.

Hakan dai na zuwa ne bayan Twitter ya goge wani sako da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa kan ayyukan ’Yan Awaren Biyafara na IPOB ranar Talata, inda Twitter ya ce sakon ya yi karan-tsaye ga dokokinsa.

A sakon na Buhari, ya kafa hujja da abin da ya faru a Yakin Basasar Najeriya sannan ya yi barazana ga masu tayar da zaune tsaye a cikin kasar. 

A jerin sakonnin Shugaban, ya ce: “Galibin masu tayar da tarzoma a yau yara ne kanana da ba su san abin da ya faru a lokacin Yakin Basasar Najeriya ba.

“Mu da muka fafata a fagen yakin na wata 30, muka shaida yakin, za mu yi maganin su ta harshen da suka fi fahimta,” kamar yadda ya wallafa.

Da da yake martani kan matakin na Twitter, Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya zargi Twitter da yin bakin ganga.

Ya ce shafin ya yi buris da sakonnin tayar da zaune tsaye da jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB Nnamdi Kanu da ’yan kanzaginsa ke wallafawa.

Ya ce Twitter ya ki daukar mataki kan sakonnin da suka tunzara kashe ’yan sanda da nuna halin ko-in-kula yayin zanga-zangar #EndSARS inda aka fake da ’yancin dan Adam wajen lalata kadarorin gwamnati da na jama’a da kuma kone-kone.  

Ministan ya ce akwai lauje cikin nadi a matakin na Twitter kuma Najeriya ba za ta lamunta ba saboda, “Twitter na da nata dokokin, amma ba na gama-gari ba.

“Idan Shugaban Kasa a ko’ina yake a duniya bai ji dadin abin da ke faruwa ba, yana da damar bayyana ra’ayinsa. 

“A yanzu ya dace mu daina kwatanta baki da fari. Idan an haramta kungiya, akwai bambanci tsakaninta da wacce ba a haramta ba. 

“Kungiyar da ke umartar mambobinta da su kai hare-hare a kan caji ofis-ofis na ’yan sanda da kashe jami’an tsaro da kai hari a gidajen yari da kashe gandurebobi, amma a ce Shugaban Kasa ba shi da ’yancin bayyana bacin ransa a kai?,” kamar yadda Ministan ya nunar.