✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na shirin kwashe ’yan ƙasarta daga Lebanon

Aƙalla ’yan Najeriya 5,000 ke zaune a ƙasar Lebanon inda ake zargin yiwuwar ɓarkewar yaƙi.

Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kwaso ’yan ƙasarta daga ƙasa Lebanon sakamakon fargabar yaƙi.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta buƙaci ’yan ƙasar mazauna Lebanon da su garzaya ofishin jakadanci da ke Lebanon domin ɗaukar bayansu da kuma kwaso su zuwa gida.

An fara fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran ne bayan harin makamai masu linzami sama da 180 da Iran kai wa Isra’ila.

Iran ta kai harin ne a matsayin martani kan kisan shugabannin ƙungiyar Hisbullah da hare-haren Isra’ila suka kashe a Lebanon.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya lashi takobin ɗaukar fansa, a yayin da Iran ta ce ta shirya, lamarin da ya sa ake fargabar ɓarkewar mummunan yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ƙasashen Saudiyya da China dai sun buƙaci manyan abokan gaban da su kai zuciya nesa.