Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kwaso ’yan ƙasarta daga ƙasa Lebanon sakamakon fargabar yaƙi.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta buƙaci ’yan ƙasar mazauna Lebanon da su garzaya ofishin jakadanci da ke Lebanon domin ɗaukar bayansu da kuma kwaso su zuwa gida.
An fara fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran ne bayan harin makamai masu linzami sama da 180 da Iran kai wa Isra’ila.
Iran ta kai harin ne a matsayin martani kan kisan shugabannin ƙungiyar Hisbullah da hare-haren Isra’ila suka kashe a Lebanon.
- Iran da Isra’ila: Saudiyya ta gana da shugaban Iran
- Najeriya ta soke harajin VAT a kan iskar gas da man dizel
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya lashi takobin ɗaukar fansa, a yayin da Iran ta ce ta shirya, lamarin da ya sa ake fargabar ɓarkewar mummunan yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ƙasashen Saudiyya da China dai sun buƙaci manyan abokan gaban da su kai zuciya nesa.